28 Satumba 2020 - 11:00
​Jerusalem Post: Kulla Alaka Tsakanin Isra’ila Da UAE Zai Amfanar Da Isra'ila Ne

Jaridar yahudawan Isra’ila ta The Jerusalem Post ta bayar da wani rahoto da ke cewa, Isra’ila za ta yi amfani da damar da ta samu ta kulla alaka da hadaddiyar daular larabawa UAE.

ABNA24 : A cikin rahoton nata, jaridar The Jerusalem Post ta bayyana cewa, UAE kasa ce mai matukar muhimmanci a yankin gabas ta tsakiya, ta fuskacin kasuwanci da harkokin tattalin arziki, da kuma baje na kwarewar kasashe a dukkanin bangarorin.

Rahoton ya ce dukkanin wadannan bangarori Isra’ila za ta yi amfani da su domin amfanin kanta, kamar yadda kuma akwai bangare guda mafi muhimmanci ga Isra’ila dangane da wannan alaka, shi ne bangaren tsaro, inda Isra’ila za ta yi amfani da alakarta da UAE domin cimma burinta ta fuskar tsaro a yankin.

Tun daga ranar da UAE ta sanar da kulla alaka da Isra’ila ‘yan makonnin da suka gabata, jami’an Isra’ila suka bayyana cewa sun iso kusa da Iran, kuma wannan dama ce ta hada karfi da karfe tsakanin Isra’ila da larabawa domin ganain bayan kasar Iran.

342/